Ministan kudi da tattalin arziki na Nijeriya, Wale Edun ya ce gwamnatin tarayya ta amince da daukar ma’aikata 3,927 a hukumar kwastam da ke yaki da fasa kwauri.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Maiwada ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, yace ministan ya bayyana haka ne a yayin taron hukumar karo na 61 a Abuja.
Ya kuma bayyana muhimmancin da hukumar ke da shi wajen samar da kudin shiga ga gwamnatin tarayya musamman ga kasafin kudin Najeriya na shekarar 2025.