Gwamnatin tarayya ta kaddamar da sufurin motoci masu amfani da iskar gas kyauta domin saukaka zirga-zirga a Abuja.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafin X shirin shugaban kasa na amfani da motocin CNG, ya nuna yadda motocin suka fara aiki a yau Litinin.
Motocin wandanda rahotanni suka ce za su yi aiki ne a cikin unguwannin birnin Abuja, da suka hada da Mararaba zuwa Eagle Square da kuma tashar mota Berger, za su yi kwanaki 40 suna sufurin kyauta.