Gwamnatin Nijeriya da Bankin Duniya za su kashe dala miliyan 600 domin inganta tituna da kasuwannin karkara
Gwamnatin Tarayya hadin gwiwa da Bankin Duniya sun ware dala miliyan 600 domin aiwatar da shirin bunkasa tituna da kasuwannin karkara (RAAMP).
Karamin ministan noma Dr Sabi Aliyu Abdulahi ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Abuja.
Ministan ya ce tsarin bayar da tallafin ya kasance dala miliyan 500 daga bankin duniya da kuma dala miliyan 100 daga gwamnatin tarayya na jihohi, inda ya kara da cewa, shirin RAAMP zai inganta harkar noma, samar da abinci, da ci gaban tattalin arziki.