Gwamnan Kano Abba Kabir-Yusuf, ya amince da daukar lauyoyi 70 aiki a jihar domin inganta harkar shari'a.
Shugaban ma’aikatan, Abdullahi Musa ne ya bayyana haka nan take bayan kammala tattaunawa ta karshe da sabbin lauyoyin da gwamnati ta dauka aiki a ranar Juma’a.
Ya ce an dauki wannan mataki ne da nufin karfafa bangaren shari’a a jihar da kuma inganta ayyukan yi wa jama’a hidima.