Gwamnatin jihar Zamfara ta nemi agajin tarayya, bayan Bello Turji ya yi barazanar kaddamar da hare-hare a wasu yankunan jihar


Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki mataki kan kasurgumin dan bindiga Bello Turji, bayan da ya yi barazanar kai hare-hare kan al'ummomin Zamfara da Sokoto.

A cikin wani bidiyo da ya fitar a ranar Laraba, Turji ya ce idan har jami'an tsaro ba su saki makusancinsa Bello Wurgi da aka kama ba to zai hana zaman lafiya a yankin.

Da yake mayarda martani kan barazanar, mai baiwa gwamnan jihar Zamfara shawara kan hulda tsakanin hukumomin gwamnati Dr Sani Shinkafi ya yi kira ga Shugaban Bola Ahmad Tinubu da ya dauki matakin gaggawa kan wannan batu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp