Gwamnan Zamfara ya musanta labarin sace mutane a karamar hukumar Maradun


A cewar kafar yada labaran ta Channels TV, Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, ya karyata rahotannin da ke cewa 'yan bindiga sun sace mutane masu yawa a karamar hukumar Maradun ta jihar. A cikin shirin tashar ta Channels mai suna POLITICS TODAY ne dai kafar yada labaran ta ce gwamna Dauda ya ce ba a a yi garkuwa da kowa ba a jiharsa a cikin watanni 6 da suka gabata.

Rahotanni da kafafen yada labarai suka ruwaito sun ce mata da yara sama da 50 ne aka sace a kauyen Kakin Dawa na karamar hukumar Maradun.

Kwanaki biyu bayan hakan, Gwama Dauda Lawal ya bayyana a gidan talabijin din,  inda ya musanta labarin da ya ce ba gaskiya bane.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar na aiki da 'yan sanda, da sojoji, da sauran jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya, kuma babu batun sulhu da 'yan bindiga a jihar.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp