Gwamnan jihar Katsina ya amince da nadin Hon Abdulƙadir Mamman Nasir a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar.
Abdulƙadir Mamman Nasir ya maye gurbin Hon Jabiru Abdullahi Tsauri wanda Shugaba Tinubu ya nada mukami a Abuja.
Kafin nadin na Hon Abdulƙadir, shi ne shugaban hukumar kula da nomar rani ta jihar Katsina wato Katsina Irrigation Authority.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Gwamnan Malam Ibrahim Kaulah Mohammed da DCL Hausa ta samu kwafi a Katsina.
Category
Labarai