Gwamnan jihar Zamfara Dauda ya ba ma'aikatan jihar 'bonus' don saukaka musu rayuwa

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da ba ma'aikatan gwamnati a jihar kaso 30% na albashinsu a matsayin wani 'hasahi' da zai rage musu radadin rayuwa.

A wata sanarwa daga shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Ahmad Aliyu Liman, ta ce karimcin bai tsaya ga ma'aikatan gwamnati kadai ba, hada 'yan fansho da suka yi ritaya daga aiki.

Sanarwar ta ce wannan karimcin na daga cikin yunkurin gwamnatin jihar na inganta rayuwar ma'aikata da sauran daukacin al'ummar jihar.

Gwamna Dauda Lawan ya bukaci ma'aikatan jihar da su mayar da biki ta hanyar jajircewa wajen aiki don gina jihar ta zarta tsara.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp