Gwamna Caleb Mutfwang |
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya nesanta kansa daga jita-jitar da ake yadawa ta cewa ya koma jam’iyyar APC.
Wannan dai na a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na Gwamnan jihar, Gyang Bere.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan wani yunkuri ne da wasu bata gari ke yi domin raba kan al'ummar jihar.
A cewar sanarwar, Gwamna Mutfwang na hada kai da gwamnatin tarayya domin ci gaban jihar Filato.
A watannin baya dai gamayyar kungiyoyin jam'iyyar APC a Arewa ta tsakiyar Nijeriya karkashin jagorancin Hon. Saleh Zazzaga ta yi ta kiran gwamnan kan ya dawo jam’iyyar APC.
Category
Labarai