![]() |
Engineer Abba Kabir Yusuf |
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya zargi jam’iyyun adawa da rura wutar rikicin siyasa a Jihar.
Gwamnan ya yi wannan zargi ne lokacin da ya ke zantawa da manema labarai yayin taron majalisar zartarwar jihar a ranar Laraba, har ma ya bayyana aniyarsa ta daukar tsauraran matakan da suka dace don dakile sake barkewar ‘yan daba a Jihar.
Wannan dai ya biyo bayan rikicin baya-bayan nan da ya barke tsakanin wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne a Kano.