Gwamna Abba Gida Gida ya zabi tsohon shugaban ma'aikatansa da wasu mutum 5 a matsayin kwamishinoni


Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya tura sunayen mutane 5 zuwa ga majalisar dokokin jihar domin ta tantancesu a matsayin kwamishinoni.

Kakakin majalisar dokokin jihar Isma'il Jibrin Falgore ne ya karanta wasikar gwamnan a zaman majalisar na yau Litinin, a cewar jaridar Dailytrust.

Mutanen da gwamnan ke son majalisa ta tantance sun hada da tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatinsa, Shehu Sagagi, da Dr Dahiru Mohd Hashim, da Ibrahim Abdullahi Wayya, da Dr Isma’il Dan Maraya, da Gaddafi Sani Shehu da kuma Abdulkadir AbdulSalam.

Wannan na zuwa ne, kwanaki kadan bayan da gwamnan ya kori sakataren gwamnati Abdullahi Bichi, tare da wasu kwamishinoni 5 tare da roshe ofishin shugaban ma'aikata.

1 Comments

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp