Mummunar gobara ta da ta tashi a kasuwar Moniya da ke karamar hukumar Akinyele a jihar Oyo, ta kone shaguna 17 ƙurmus, lamarin da ya haddasa asarar miliyoyin kudade.
Gobarar wadda ta faro da misalin karfe 12 da minti 30 na daren ranar Lahadi, ana kyautata zaton wutar lantarki ce ta haddasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito
Rahotanni sun bayyana cewa, gobarar ta yi barna sosai, tare da lalata kayayyaki masu daraja baya ga makudan kuɗaɗe da laƙume.
Wasu da gobarar ta yi wa barna; Yetunde Musa da Ajetunmobi Idowu da Olaide Badmus da Balogun Sulaimon da kuma Ajetunmobi Kolawole, sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta tallafawa wadanda abin ya shafa domin rage musu radadin asarar da suka tafka.
Category
Labarai