Gidan Talabijin mai zaman kansa na farko a Nijeriya ya dakatar da aikinsa


Masu gidan talabijin mai zaman kansa na farko a Nijeriya DITV da Alheri Radio, wanda shi ne gidan rediyo mai zaman kansa mafi tsufa a arewacin Nijeriya, sun sanar da dakatar da ayyukansu sakamakon rashin kudin gudanarwa da matsin tattalin arziki ta haifar. 

A wata sanarwa da mukaddashin shugaban gidan talabijin din Idris Mustapha, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan aiki musamma lantarki, ya sa ba zasu iya ci gaba da gudanar da aiki ba kamar yadda ya kamata ba. 

Sanarwar ta kuma ce, bangaren gudanarwar kafofin na fuskantar karancin kudi, sakamakon janyewar wasu ‘yan kasuwa da a baya ke bayarda talla a gidan Talabijin din.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp