Gidajen mai na NNPC sun rage farashin fetur zuwa 965 a Abuja
Farashin man fetur ya ragu zuwa Naira 965 kan kowace lita a gidajen mai na kamfanin NNPCL da ke babban birnin tarayya Abuja.
Majiya DCL Hausa ta jaridar PUNCH ya nuna cewa kamfanin man fetur na Najeriya ya sanya sabon farashi a gidajen man sa na babban birnin kasar
Wannan sabon farashin dai shi ne karo na biyu cikin makonni biyu, inda a baya ya sauka zuwa N1,060 a farkon wannan wata.
A Gidan man NNPCL dake Wuse Zone 4, Olusegun Obasanjo Way, Central Area, ana siyar da man a farashin Naira 965 ga kowace lita inda matafiya ke yunƙurin shiga cikin layi don sayen mai.
Category
Labarai