Gazawar gwamnati wajen magance yunwa ne ya haifar da turmutsutsi a rabon abinci - Bishop Mathew Kuka



Jagoran Cocin Katolika a jihar Sokoto, Bishop Mathew Hassan Kukah ya dora alhakin turmutsutsin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane a jihohin Oyo da Anambra da babban birnin tarayya Abuja akan gazawar gwamnati wajen magance matsalar yunwa da ta addabi kasar.

Ya kuma koka akan yadda Nijeriya ke ci gaba samun koma baya shekaru 60 bayan samun 'yancin kai.

A cikin sakonsa na bukin Kirsimeti, Bishop Kukah ya nuna damuwarsa akan yadda matasa ke shan wahala domin tsayawa takara saboda yawan kuɗaɗen da ake kashewa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp