Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya taya shugaban jam'iyyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje murnar cika shekaru 75 a duniya.
Shugaban ya jinjinawa irin jagoranci da kudirin Ganduje na ciyar da jihar Kano da ma Nijeriya a gaba.
A cikin wani sako da mai magana da yawunsa ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma yaba da irin gudunmawar da Ganduje ke bayar wa wajen ci gaban jam'iyyar APC da kuma tsare tsaren gwamnati.