Gwamna Ahmadu Fintiri |
Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya sanar da kafa sabbin masarautu bakwai a jihar.
Sabbin masarautun sun hada da masarautar Huba da Madagali da Minchika da Fufore sai Gombi da Yungur da kuma Maiha.
A cewar gwamnan, masarautun Huba da Madagali, da Minchika, da Fufore za su kasance masarautu masu daraja ta biyu, yayin da masarautun Gombi, da Yungur da Maiha za su kasance masu daraja ta uku.