Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari |
Malam Garba Shehu, mai magana da yawun tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya magantu game da labarin da ake yadawa cewa an kwace filin mai gidansa a Abuja.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Garba Shehu, ya ce Buhari ba shi ne mai wannan filin da ake magana ba, an bayar da shi ga gidauniyar Muhammadu Buhari.
A baya-bayan nan ne wasu sunaye sama da 700 suka fita cewa ministan Abuja ya kwace takardun filayen ciki har da tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.