Farashin wake da taliya ya sauka a wasu kasuwannin Nijeriya


Shinkafar waje ta kusa kullewa dubu 100 a kasuwar Giwa jihar Kaduna, inda ake sayar da ita 99,000, 

A kasuwar Mai'adua jihar Katsina naira 97,000 ne kudin buhun shinkafar waje a satin nan, an samu karin naira 9,000 kan yadda aka saida a makon da ya shude   88,000.

Sai dai farashin bai karu ba a kasuwar Dandume da ke jihar Katsina a makon nan, da ake saidawa  N85000 haka aka saida tun a makon da ya gabata.

N85,000 - 90,000 ake sayarda buhun shinkafar waje a kasuwannin jihar Adamawa a wannan mako, banbancin kadan ne da na satin da ya wuce da aka saya 
N87,000 - 90,000.

A kasuwar Mile 12 International an samu karin dubu uku kan buhun shinkafar waje inda ake saida ita 90,000, sabanin 87,000 da aka saida a makon da ya gabata.

SHINKAFAR HAUSA

Shinkafar Hausa ta fi tsada a kasuwannin jihar Adamawa, N160,000 ake sayarda buhu a wannan makon, inda a makon jiya take N140,000 zuwa 145,000.

A wannan makon ₦155,000 ake sayarda shinkafar Hausa a kasuwar Giwa jihar Kaduna da kasuwar Mile 12 International Market, haka farashin yake a makon jiya.

A kasuwar Mai'adua jihar Katsina farashin shinkafar ya kai naira N140,000 zuwa 145,000 inda a makon da ya shude aka saida N138,000.

A Can  kasuwar Dandume, mako na biyu kenan farashin bai sauya ba, ₦140,000 zuwa ₦160,000 ake sayar da shinkafar hausa a kasuwar. 

Shinkafa Shanshera kuwa  N55,000 zuwa N58,000 ake saidawa a kasuwar Saminaka jihar Kaduna a makon nan, a makon da ya shude kuwa  N50,000-55,000 ake sai da buhunta.

WAKE

Farashin wake ya kara saukowa a kasuwar Mile 12 International inda ake sayarda tsohon wake naira 200,000 sabanin 210,000 da aka sayarda buhun a baya, sabon wake kuwa naira N180,000 .

A kasuwannin jihar Adamawa farashin wake ya yi tashin gwauron zabi, a wannan mako N155,000 zuwa 160000 ake sayarda buhun manyan wake, sai dai a makon da ya shude N120,000 aka saida buhun kananan wake  a kasuwar. 

A kasuwar Dandume  jihar  Katsina  ₦90,000 zuwa ₦115,000 ake sayarda buhun kananan wake a makon nan, a satin da ya gabata  N90,000-140,000 aka sai da.

Naira 120,000 ake sayarda buhun wake a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a wannan mako.

Farashin bai sauya zani ba a kasuwar  Saminaka  jihar  Kaduna, wanda ake sai da buhun wake N110,000-120,000 sati biyu da suka gabata

Amma a kasuwar Giwa jihar Kaduna an samu saukin N10,000, inda a makon nan ₦105,000 ake saida buhu, a satin da ya shude  kuwa  N115,000 aka sai da buhun wake.

MASARA

Farashin masara a kasuwar Mai'adua ya sauka daga naira 69,000 a makon da ya shude zuwa naira 66,000 - 67,000 a wannan mako, haka farashin yake a kasuwannin jihar Adamawa.

Ana sayar da buhun masara  ₦50,000 zuwa ₦60,000 a kasuwar Dandume jihar Katsina a satin nan, haka farashin yake a makon jiya.

N60,000 ake sayar da masara a kasuwar Giwa jihar Kaduna a makon nan, yayinda a makon jiya aka sai da N64,000, an samu sauƙin Naira 4000 kenan.

Can ma a Saminaka farashin ya sauka, inda ake sayar da masarar Naira 52,000 - 55,000 a wannan mako, a makon jiya kuwa N55,000 zuwa 57,000 aka saida.

A kasuwar Mile 12 farashin tsohuwar masara ya sauka inda ake sayar da buhunta 95,000 a wannan makon, yayinda a makon da ya wuce aka saidai 105,000, an samu sauƙin 10,000 kenan a satin nan.

Farashin sabuwar masara bai sauya ba yana nan N90,000 a kasuwar Mile 12.

TALIYA

Bari mu karkare da farashin kayan abincin da  taliya, wadda ke ci gaba da yin sauki a kasuwannin Nijeriya.

A wannan makon ana sayar da kwalin taliya N20,000 a kasuwar Dandume  jihar Katsina, yayinda a satin da wuce aka saida 22,000.

19,500 taliya take a Kasuwar Giwa jihar Kaduna a makon nan, sai makon da ya shude aka  saida  N20,000.

Farashin bai sauya ba a kasuwar Mile 12 International da ke Lagos wanda aka saida  N21,000 hakama a jihar Adamawa farashin yana nan kan N19700 da aka saida a makon da ya gabata. 


To a kasuwar  Mai'adua  jihar Katsina  N18000 ake saida kwalin taliyar Spaghetti  a makon nan.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp