Gabanin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, farashin tikitin jirgin sama a cikin gida Nijeriya ya yi tashin gwauron-zabi yayinda wasu kamfunnan aka saye tikitin musamman a yankunan Kudu-maso-Gabas da Kudu maso Kudu
Majiyar DCL Hausa ta Daily trust ta rawaito cewa farashin jirgi a yankunan ya karu da sama da kashi 100 inda ake sayar da tikitin tsakanin N380,000 zuwa N500,000.
A ranar Juma’ar da ta gabata an lura da cewa babu tikiti a jirgin Legas zuwa Fatakwat a kamfunnan Ibom Air, ValueJet da kuma tikin Arik Air.
Wani fasinja, Mista Kelechi Okpara, wanda ya ce ya samu jirgi zuwa Owerri amma a farashin N500,000 daga Lagos.