Mazauna birnin Kano na ci gaba da nuna damuwa sakamakon sake dawowar fadan daba inda a kwanannan fada ya kaure bayan wasar kwallon kafa da ta gudana filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata.
Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayinda 'yan daba dauke da muggan makamai su ka riƙa fasa shaguna tare da kwace wayoyi da dukiyar mutane a unguwannin Zango Quarters da Yakasai kusa ga Kasuwar Rimi.
Wani mazaunin Yakasai Umar Tijjani from, ya ce suna cikin dar-dar na yiyuwar ramuwar gayya, abinda ya sa mutane ke shigewa gidajensu ana kammala sallar Isha.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Salman Dogo wanda ya ziyarci unguwannin ya sha alwashin tabbatar da doka da oda tare da yaki da daba a jihar Kano.