Mutane 23 da EFCC ta kama bisa zargin damfara ta intanet |
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC ta kama wasu mutane 23 da ake zargi da yin damfara ta intanet a yankin Akobo da ke Ibadan a jihar Oyo.
Jami’an hukumar ta EFCC shiyyar Ibadan ne suka kama wadanda ake zargin, biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba a shafinta na X, ta ce yayin samamen jami'an sun kuma kwato wasu kayayyaki da ake kyautata zaton an siye su da kudaden haramun ne.
Kayayyakin da suka hada da manyan motoci na alfarma guda takwas da na'urori sai wayoyin hannu da sauransu.
Category
Labarai