Dangote ya mayar da martani ga kamfanin NNPCL kan bashin dala biliyan 1

Aliko Dangote 

Matatar mai ta Dangote ta yi karin haske kan hadin gwiwarta da kamfanin mai na Nijeriya NNPCL, inda ta bayyana cewa ta amince da sayar da hannun jarin kashi 20 cikin 100 kan kudi dala biliyan 2 da miliyan 76.

Matatar ta Dangote ta yi karin haske ne, bayan wata sanarwa da aka fitar cewa kamfanin NNPCPL ya samu rancen dala biliyan daya domin tallafawa aikin matatar ko da za ta fuskanci wasu matsalolin kudi.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba babban jami'in yada labarai a matatar, Anthony Chiejina, ya bayyana maganar a matsayin yaudara, yana mai cewa daga cikin dala biliyan 2 da miliyan 76, an amince da cewa NNPCL zai biya dala biliyan 1 ne kawai yayin da zai biya sauran a tsawon shekaru 5 ta hanyar cire danyen man da suke samarwa matatar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp