Daliban jami'ar Abuja sun yi watsi da sauya sunan jami'ar zuwa jami'ar Yakubu Gowon da gwamnatin tarayya ta yi tare da kira a gaggauta janye wannan mataki.
Daliban sun yi wannan kira ne a lokacin da su ka fito bakin kofar shiga jami'ar jiya Alhamis, rike da kwalaye da ke nuna cewa a bar jami'ar da tsohon sunanta, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.
Da yake jawabi a madadin kungiyar daliban Comrade Nkem Silas, ya nemi gwamnatin tarayya ta janye matakin saboda ɗaliban ba sa goyon bayan haka.
Category
Labarai