Daga sama ya kamata a soma yaki da cin hanci da rashawa in har ana son samun nasara - Obasanjo

Cif Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce idan har ana son yakin da ake yi da matsalar tsaro ya yi nasara dole sai an fara da manyan jami'an gwamnati.

Obasanjo ya ce magance rashawa daga sama zai zama izina ga wasu tare da tabbatarda adalci da kuma aiwatar da ayyukan gwamnati a bude.

Shugaban wanda ke magana a cikin wani shiri na wani gidan radio mai zaman kansa a Abeokuta, jihar Ogun, ya ce matsalar cin hanci da rashawa ta shiga kowane lungu kuma har sai an fara da manyan shugabanni za a samu nasara.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp