Gwamna Dauda Lawal na Zamfara, ya ce wasu jihohi da ba sa tara kudaden shiga masu yawa za su durkushe idan aka aiwatar dokar haraji da ke gaban majalisar kasa.
Gwamnan ya ce idan aka zartar da dokar harajin zai yi wahala wasu gwamnoni su iya biyan mafi ƙarancin albashin 70,000 ga ma'aikata.
Wannan dokar haraji da shugaban kasa Bola Tinubu ke son aiwatarwa na ci gaba da shan suka daga kowane lungu da sako na kasar.