Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Cole Palmer ya kafa sabon tarihi a gasar Firimiyar Ingila, inda ya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a bugun fanareti a tarihin gasar.
Dan wasa Palmer ya kafa sabon tarihin ne, a wasan da Chelsea ta samu nasara da ci 4 da 3 a kan Tottenham, inda ya zura kwallaye biyu a bugun daga kai sai mai tsaron gida da suka zama cikamakin kwallaye 12 na bugun fanareti a jere.
Wannan bajinta ta zarce ta fitaccen dan wasa Yaya Toure, wanda a shekarar 2010 ya zura wa kungiyar Manchester City kwallaye 11 a jere a bugun daga kai sai mai tsaron gida ba tare da ya zubar ba.