Buhun albasa ya doshi N250,000 |
Wani zagaye da Jaridar Dailytrust ta yi a wasu kasuwannin kayan miya a manyan birane ya gano cewa farashin albasa ya yi tashin gauron zabbi.
Wakilin Jaridar a jihar Kano ya rawaito cewa ana siyar da babban buhun albasa akan kudi Naira dubu 250, wanda a shekarar da ta gabata ana siyarwa akan naira dubu 120, yayin da tsakatsakin buhu kuma ake siyarwa akan naira dubu 180, maimakon naira dubu 80 da ake siyarwa a bara.
A Jos babban birnin jihar Plateau ma, haka farashin yake inda ake siyar da babban buhun akan naira dubu 250, yayin da rabin buhu kuma ake siyarwa akan naira dubu 125.
Akwai kuma wasu kalolin albasar da ake siyar da farashin babban buhun yana farawa ne daga naira dubu 215 zuwa dubu 230.