Bello Turji tamkar gawa ce ke tafiya - Hedikwatar tsaron Nijeriya


Bello Turji 

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta bayyana cikakken ‘yan bindigar nan mai suna Bello Turji, a matsayin gawa ne ke tafiya.

Wannan dai ya biyo bayan barazanar da kasurgumin dan bindigar ya yi na kai farmaki ga al’ummomin jihar Zamfara.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a cikin wani sabon faifan bidiyo da Bello Turji ya saki Turji kalubalantar sojojin Nijeriya, inda ya zarge su da kama 'yan uwansu tsofaffi tare da neman a sako abokinsa Bako Wurgi da jami'an tsaro ke tsare da shi.

Ya kuma yi barazanar kai hari a sabuwar shekara mai kamawa ta 2025 matukar ba a biya masa bukatunsa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp