Banyi nadamar cire tallafin man fetur ba – Tinubu

Shugaba Tinubu 

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa bai yi nadamar cire tallafin man fetur ba a kasar.

Shugaban ya fadi hakan a ranar litinin lokacin da yake tattaunawa da kafafen yada labarai, ya ce cire tallafin man fetur ya zama dole domin hana kasar fadawa cikin mawuyacin hali.

Idan zaku tuna a baya Shugaba Tinubu a lokacin da yake rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu 2023, ya sanar da cire tallafin man fetur nan take, yanayin da ya kawo tsadar rayuwa a kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp