Bankunan Nijeriya sun kara adadin kudin da za a iya cirewa zuwa dubu 50 a kowace rana

Bankunan ajiya a Abuja babban birnin Nijeriya sun kara yawan adadin kudaden da abokan hulda za su iya cira zuwa Naira dubu 50 a kowace rana. 

Wani bincike da jaridar PUNCH ta gudanar a ranar Talata ya nuna cewa bankunan da suka hada da GT da Zenith sun kara adadin daga Naira dubu 5 da aka sani a watan da ya gabata zuwa dubu 50. 

Yanzu haka dai abokan hulda suna da damar cirar Naira dubu 50 a cikin banki, ko Naira dubu 20 a na'urar cirar kudi.

Wani jami’in bankin GT a Abuja da ya zanta da jaridar PUNCH ya ce a yanzu haka akwai wadataccen kudi a bankin dalilin da ya sanya aka kara adadin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp