Bankin duniya ya hannanta wa Nijeriya bashin dala bilyan 1.5 don ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren tattalin arziki


Bankin duniya ya hannunta wa gwamnatin Nijeriya bashin dala biliyan 1.5 domin ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren tattalin arzikin kasar da su ka haɗa cire tallafin man fetur da garambawul ga dokar haraji.

Bankin dai ya amince da baiwa kasar bashi har kashi biyu da ya haɗa da dala biliyan 1.5 da kuma dala miliyan 750.

Lamunin na da manufar taimaka wa Nijeriya aiwatar da tsare-tsaren tattalin arziki da su ka da habbaka hanyoyin shigar kudade ga kasar baya ga bangaren man fetur, aiwatar da kasafin kudi da kuma wasu ayyuka na ci gaban al'umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp