Babban sufetan 'yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun, ya ce bangaren shari'a na kasar nan ya yi rauni kuma yana bukatar sauye-sauye.
Ya kuma yi kira da 'yan Nijeriya su daina zargin 'yan sanda da zama matsala a kasar.
Babban Sufetan wanda ya samu wakilcin mai magana da yawun rundunar ACP, Muyiwa Adejobi a wurin taron kungiyar masu dauko labarin miyagu laifukka, ya ce ba 'yan sanda ne kawai bangaren doka na kasar dake fuskantar matsaloli ba, sai dai suna kokarin gyara tsarin.
Category
Labarai