Jagoran darikar Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ƙaryata rade-radin da ake yaɗawa cewa madugun adawa a Nijeriya Atiku Abubakar da na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar LP, sun kulla wata yarjejeniyar siyasa.
A cikin wata hira da BBC, tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya ce bai da wata masaniya kan labarin amma ya ji rahotannin dake cewa magoya bayan Atiku na ci gaba da tuntubar dattawa da malamai akan wannan batu.
Kwankwaso ya nuna ɓacin ransa akan yadda wasu manyan mutane da ake ganin girmansu ke yada irin wadannan labarun da ba su da tushe balle makama.