Ba za ka iya janyo Nijeriya cikin faɗanku da Faransa ba - Martanin Ribadu ga Janar Tchiani


Mai baiwa shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana zarge-zargen shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Tchiani a matsayin marasa tushe.

A cikin wata fira da gidan talabijin na Nijar RTN ya yaɗa, Tchiani ya zargi Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da haɗa baki da Faransa wajen yi wa Nijar zagon kasa.
 
A martanin da ya mayar cikin wata hira da kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa, Malam Nuhu Ribadu ya ce saboda kawai Nijar na takun saka da Faransa, bai zama dole Nijeriya ta shiga faɗan ba ko daukar bangare.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp