Wasu sassan babban birnin tarayya Abuja na cikin matsalar rashin wutar lantarki saboda lalata layin wuta 330-kilovolt Shiroro-Katampe da barayi su ka sake yi.
Wani bayani da mai magana da yawun kamfanin samarda lantarki na Nijeriya Ndidi Mbah ya fitar, ya ce wutar ta lalace ne sun da misalin 11:43 na dare.
Mbah ya kara da cewa tuni aka tura jami'ai zuwa wurin da wutar ta lalace domin sauya injimin da aka lalata.
Category
Labarai