Sanata mai wakiltar yankin Borno ta Kudu a majalisar dattawan Nijeriya Mohammed Ali Ndume, ya ce yankin arewa ba ci-ma-kwance ne ba ta fannin samar da tattalin da yankin zai dogara da shi.
Ndume wanda ya bayyana haka a cikin wani bayani da ya fitar a jiya, ya ce kowane yanki na kasar na bukatar wani domin rayuwa duk kuwa arzikin da ya tara.
Tsohon jagoran majalisar dattawan na mayar da martani ne kan wasu kalamai da ake jifar arewa da su cewa, yankin ba zai iya dogara da kansa ba saboda 'yan yankin ba su biyan haraji.