Yara ƙanana 35 ne aka tabbatar da mutuwar su sakamakon wani turmutsitsi da ya faru a wurin wani shagali da ya gudana a unguwar Orita Bashorun, dake birnin Ibadan na jihar Oyo
Rundunar 'yan sandan jihar ta ce akwai wasu mutum 6 da suka samu rauni kuma a ke ci gaba da kula da lafiyar su a asibiti.
A cikin wani bayani da kakakin rundunar Adewale Osifeso ya fitar, ya ce an kama mutane 6 da ake zargin suna da hannu a wannan hatsarin da ya faru. Daga cikinsu akwai tsohuwar matar Ooni na Ile-Ife Naomi Silekunola, da shugabar makarantar Islamic High School, Ibadan, da sauransu.