Asibitin tarayya dake Asaba jihar Delta ta yi nasarar yi wa yara mata biyu da aka haifa ba tare da dubura ba tiyata.
Aikin wanda aka shafe sa'o'i ana yi, an budewa yaran 'yar shekara 7 da 'yar shekara 1, hanyar da za su iya yin bahaya.
Shugaban asibitin Dr. Victor Osiatuma, ya bayyana wannan a matsayin wata babbar nasara ga asibitin.