Tambarin Kotun da'ar ma'aikata |
Har yanzu tsugune ba ta kare ba a kotun da’ar ma’aikata ta Nijeriya CCT yayin da ake takun-saka tsakanin shugabanta, Danladi Umar da sabon shugaban da aka nada, Mainasara Kogo, waɗanda ko wannensu ke ayyana kan sa a matsayin shugaba.
Binciken da jaridar Dailytrust ta yi ya nuna cewa mutanen biyu ko wanne ya je ya tattaunawa da ma’aikatan kotun ba tare da wani kwakkwaran umarni kan wane ne shugaba ba.
A ranar 13 ga watan Yuli ne shugaba Bola Tinubu ya nada Kogo a matsayin sabon shugaban kotun ta CCT, kazalika a wannan rana ce ya bayyana Omolola Oloworaran a matsayin Darakta Janar na Hukumar Fansho ta Kasa wato PENCOM.
Su dai ma’aikatan sun koka kan yadda ake tafiyar da aikin kotun tun bayan da aka fara cece-ku-ce kan batun tsige Danladi Umar.