An samu ma'aurata mafi tsufa a duniya

Bernie Littman mai shekara 100, da Marjorie Fiterman mai shekara 102 sun angwance. 

Wani rahoto da kundin tarihi na duniya ya fitar a ranar Talata ya nuna cewa, yanzu haka sun zama ma'aurata mafi tsufa a duniya. 

Rahotanni sun bayyana cewa a baya dai, sun taba yin aure sama da shekaru 60, har abokan zamansu suka mutu, kafin daga bisani yanzu su sake angwancewa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp