Karamar hukumar Garun Malam a jihar Kano ta sanar da rufewa nan take kasuwar sayar da tumatir ta Kwanar Gafan bisa zargin aikata alfasha a cikin kasuwar.
Daga cikin alfashar da ake zargin aikatawa akwai batun namiji na neman namiji dan'uwansa da ma batun karuwanci.
Shugaban karamar hukumar Garun Malam Barr. Aminu Salisu Kadawa, ne sanar da hakan ga majiyar DCL Hausa ta jaridar Daily Trust.
Ya ce duk wanda ke kasuwar, an shi nan da 1 ga watan Janairun 2025 mai kamawa.