Tambarin NBS |
Hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS ta sanar da cewa wasu batagari sun yi wa shafinta na intanet kutse.
Hukumar ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka wallafa a shafinta na X ranar Laraba, inda ta bukaci jama’a da su yi watsi da duk wani bayani ko rahoton da aka gani a shafin, har sai an shawo kan matsalar.
Hukumar ta baiwa jama'a tabbacin cewa tawagar kwararrunta na aiki tukuru domin kwato shafin daga hannun batagari.