Fadar gwamnatin Nijeriya ta ce matatar mai ta Fatakwal ta biyu, mai karfin tace ganga 150,000 na danyen mai a kowace rana za ta soma aiki nan bada jimabawa ba.
A kwanakinnan ne matatar Fatakwal dake tace ganga 60,000 rana ta soma aiki yayinda ake ci gaba da gyaran dayar matatar wadda ta fi girma.
Wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasa Bayo Onanuga ya fitar, ya bukaci 'yan Nijeriya su yi watsi da kalamai marasa kyau da ake yadawa kan sabuwar matatar da ta fara aiki.
Duk da cewa matatar ba ta aiki kashi 100, amma kashi saba'in yana aiki yadda ya kamata, inji Bayo Onanuga.
Category
Labarai