An kulle filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja ta wucin gani, bayan wani hadari da ya faru lokacin da jirgin kamfanin Allied ke kokarin sauka.
Rahotannin sun ce tayar jirgin ce ta fashe sai ya sauka akan hanya, lamarin da ya sa aka dakatar da sauka da tashin jirage har sai an dauke jirgin.
Hukumar kula da filayen jiragen sama na Nijeriya ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce babu wanda ya same mutane 5 da jirgin ke dauke da su.