An kakkaɓe Lakurawa a Najeriya – Ministan tsaro Bello Matawalle

 

Ministan kasa a ma'aikatar tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa an fatattaki Kungiyar lakurawa daga Nijeriya

Bello Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa dake Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Ya uma yi watsi da maganar kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Zamfara Mohammed Shehu Dalijan, wanda ya yi zargin cewa ‘yan Kungiyar ta  Lakurawa ne ke da alhakin tada bama-baman da suka hallaka mutane da dama a jihar makonnin da suka gabata.

Kungiyar, wadda ta fara bulla a tsakanin shekarar 2016 ko 2017 a jihar Sakkwato, ta fara ne a matsayin kungiyar kare kai dake kare al'ummar da yan bindiga da suka addaba a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp