Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce ta gurfanar da wasu 'yan kasar waje 113 da laifukan da suka shafi yanar gizo, wadanda suka hada da zamba da safarar kudade da dai sauran su.
Wani bayani da mai magana da yawun rundunar ya wallafa a shafinsa na X, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ofishin rundunar 'yan sanda mai yaki da laifukkan yanar gizo ne ya kama mutanen a ranar 3 ga watan Nuwamban 2023 a birnin tarayya Abuja.
Wadanda aka kama a yayin sammen, na fuskantar zarge-zarge ciki har da wadanda suka shafi shige da fice da kuma safarar bil adama.