Amnesty International ta yi zargin mutuwar mutune 10,000 dake tsare a hannun sojojin Nijeriya

 


Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi zargin cewa mutane 10,000 sun mutu tsare a hannun sojojin Nijeriya tun bayan da yaki ya barke a yankin arewa maso gabas.

Daraktan hukumar a Nijeriya Isa Sanusi ne ya bayyana hakan, a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Maiduguri.

A cewarsa, jami'an sojin Nijeriya sun saba dokoki harbi da kuma tsare al'umma ba bisa ka'ida ba, lokacin da suke yaki da kungiyar 'yan ta'addan da ta addabi yankin tafkin Chadi.

Amnesty International kuma ta zargi gwamnatin Nijeriya da kasa gudanar da bincike domin hukunta wadanda ake zargi da aikata wannan aika-aikar kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.

Sai dai a martanin da ta mayar, hedikwatar tsaron Nijeriya, a cikin wata sanarwa da Kakakinta Major General Edward Buba ya fitar, ta musanta zarge-zargen na Amnesty International.



Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp