"Allah Ya kiyaye Tinubu ya yi mulki karo na biyu" - Martanin Atiku ga George Akume


Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya mayarwa sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume martani, akan cewar 'yan siyasar arewa su jira har shekara ta 2031 domin neman kujerar shugaban kasa.

Atiku, wanda shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben shekara ta 2023, ya ce Shugaba Tinubu bai cancanta a bashi damar sake jagorancin kasar ba.

A ta bakin mai magana da yawunsa ''Shugaba Tinubu ya bata-rawarsa da tsalle"

Ya jaddada cewa 'yan Nijeriya ne za su yanke shawarar wanda zai zama shugaban kasa a shekara ta 2027.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp