Gwamnatin mulkin sojin kasar Guinea ta ce akalla mutum 56 sun mutu sakamakon wani mummunan turmutsitsi da ya faru a N’Zerekore, birni na biyu mafi girma a kasar.
Sanarwar da sojojin suka fitar ta ce turmutsitsin ya faru ne sanadiyar wani rikici tsakanin magoya bayan kwallon kafa da aka gudanar jiya Lahadi, lamarin da ya janyo hasarar rayukan mutane da dama.
Kafofin yada labarai na kasar Guinea sun ruwaito cewa an shirya wasar ne domin murnar zagayowar ranar da shugaban mulkin sojan kasar Mamadi Doumbouya ya yi juyin mulki tare da nada kan sa a matsayin shugaban kasa.